Gidauniyar Rubicon ta kaddamar da aikin tallafin kiwon lafiya a Ribadu

A kokarin kare lafiya da walwalar Al’ummar Ribadu, wata kungiya mai zaman kanta karkashin gidauniyar ‘Rubicon Foundation’ ta bayar da tallafin kiwon lafiya kyauta ga mazauna gundumar Ribadu da ke karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa.
Aikin kula da lafiya na kwana daya da aka gudanar a ranar Juma’a na da nufin inganta lafiyar jama’a da tallafawa iyalai marasa galihu wanda ya hada kwararrun likitoci, masu sa kai domin ceton rayuka.
Da yake jawabi a wurin taron, wanda ya kafa gidauniyar, Barista Ahmad Nuhu Ribadu ya sake nanata manufar gidauniyar na inganta rayuwa ta hanyar samun kulawar lafiya, ilimi, da kuma karfafa tattalin arziki.
Barista Ribadu ya bayyana cewa, kudirin gidauniyar Rubicon na isa ga al’ummomin da ba su da galihu da kuma magance manyan kalubalen zamantakewa da lafiya a fadin yankin yana kira ga dukkan mutane da su goyi bayan kokarin inganta al’umma da kewayenta.
Shugabannin al’umma da wadanda suka amfana sun nuna matukar godiya ga ayyukan jin kai da Gidauniyar ke gudanarwa akai-akai, suna bayyana shirin a matsayin wanda ya dace kuma mai tasiri.
