Zaɓen shugaban Kamaru: Magoya bayan ƴan adawa na ci gaba da zanga-zanga

Magoya bayan babban ɗan’adawa a Kamaru Issa Tchiroma Bakary sun sake fitowa kan wasu titunan birnin Garwa da ke arewacin kasar inda suke zanga zanga a yayin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasar.
A gobe Alhamis ne ake sa ran sanar da sakamakon zaben inda sakamakon farko-farko da ke fitowa ke nuna cewa shugaban kasar mai ci Paul Biya ne ke kan gaba.
Masu zanga zangar dai na kiran da ayi adalci wajen sanar da wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasar.
Yau Laraba ne ya kamata a ce dokar hana hawa babur ta fara aiki a wasu biranen ƙasar, musamman Garoua.
Hakan na zuwa ne sakamakon arangama da aka samu tsakanin magoya bayan Issa Tchiroma Bakary da jami’an tsaro a ranar Talata.
Hakan ya biyo bayan korafe-korafen jam’iyyar adawa kan yadda aka gudanar da zaben, inda suke zargin cewa gwamnati na ƙoƙarin murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ƙasar.
A garin Garoua na arewacin kasar, an kama aƙalla masu zanga-zanga 20 a ranar 21 ga Oktoba, kuma ana sa ran za su fuskanci shari’ar soji bisa laifin tada tarzoma da rikici, in ji Ministan Gudanar da Harkokin Cikin Gida, Paul Atanga Nji.
A kokarin daƙile rikice-rikicen, hukumomi a sashin Menoua na yammacin Kamaru sun haramta duk wasu zanga-zangar jama’a da tafiye-tafiye da hawa babur da kuma sayar da mai a kwalabe tun daga ranar 21 ga Oktoba har zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba.
