Masu gangami kan sakamakon zaɓe sun yi arangama da ƴansanda a Kamaru

0
1000236861
Spread the love

Masu gangani sun bazama a titunan biranen Garoua da Yaounde na ƙasar Kamaru, inda suke neman hukumar zaɓe ta fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar daidai da yadda suka kaɗa ƙuri’unsu.

A ranar 12 ga watan Oktoba ne al’ummar Kamaru suka je rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa, karo na farko da aka samu zazzafar adawa a tsawon shekaru.

Sai dai tun bayan zaɓen ake ci gaba da zaman ɗarɗar, bayan artabun da aka samu tsakanin magoya bayan ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary da jami’an tsaro a ranar zaɓe da kuma ikirarin nasar da ɗan takarar na adawa ya yi.

Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ɗaruruwan mutane ke tarwatsewa yayin da ‘yansanda ke watsa musu barkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu gangamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *