FAAC: Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba Naira tiriliyan 2.103 na watan Satumba

Kwamitin rar’bon arzikin ƙasa na tarayya (FAAC) ya raba jimillar kuɗaɗen watan Satumba 2025 da suka kai Naira tiriliyan 2.103 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
An gudanar da taron rarraba kuɗaɗen a watan Oktoba 2025 a birnin Abuja, inda aka bayyana cewa kuɗaɗen sun haɗa da Naira tiriliyan 1.239 na kuɗaɗen doka, Naira biliyan 812.593 daga harajin ƙarin kuɗi (VAT), da kuma Naira biliyan 51.684 daga harajin mu’amalar kuɗi ta lantarki (EMTL).
Bayanan da kwamitin FAAC ya fitar sun nuna cewa jimillar kuɗin da aka tara gaba ɗaya a watan Satumba ta kai Naira tiriliyan 3.054, inda aka cire Naira biliyan 116.149 don kuɗin tattarawa, sannan aka ware Naira biliyan 835.005 don tallafi, da tanadi.
Gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 711.314 daga wannan rabon, yayin da jihohi suka karɓi Naira biliyan 727.170. Ƙananan hukumomi kuwa sun samu Naira biliyan 529.954, yayin da Naira biliyan 134.956 (wanda ke wakiltar kashi 13 cikin 100 na kuɗin ma’adinai) aka bai wa jihohin da ke amfana.
Daga cikin kuɗaɗen, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 581.672, jihohi suka karɓi Naira biliyan 295.032, yayin da ƙananan hukumomi suka samu Naira biliyan 227.457.
Haka kuma, daga harajin kayayyaki na (VAT), gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 121.889, jihohi Naira biliyan 406.297, sai ƙananan hukumomi Naira biliyan 284.408.
A bangaren harajin mu’amalar kuɗi ta lantarki (EMTL), gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 7.753, jihohi Naira biliyan 25.842, yayin da ƙananan hukumomi suka karɓi Naira biliyan 18.089.
Rahoton ya nuna cewa a watan Satumba 2025, kudaden shiga daga harajin shigo da kaya, harajin (VAT) da harajin mu’amalar kuɗi ta lantarki (EMTL) sun ƙaru sosai, yayin da kudaden harajin kamfanoni da wasu haraji suka ragu.
