Coci da masallatai yanzu daya suke a Kaduna a karkashin Gwamna Uba Sani – Shugaban APC, Yilwatda

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya hada kan jihar bisa yadda ya baiwa al’ummar jihar dama ta hanyar kawar da matsalolin kabilanci da addini.
Da yake magana a Kaduna ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar APC ya ce masallatai da coci-coci yanzu haka daya suke a karkashin gwamnatin Sani.
Ya ce: “Mai girma gwamna, ina so in gode maka da ka yi wani abu na daban a Jihar Kaduna, Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wajen rashin tsaro, amma yanzu labarin ya canza.
“Na gode da yadda kaga kimar rayuwar jama’a tare da hada kan jihar Kaduna, ka kawar da matsalolin addini da kabilanci, ka baiwa kowa damar magana.
