An gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin Trump a Amurka

0
1000232210
Spread the love

Dubban mutane ne suka shiga zanga-zanga a sassan Amurka ta adawa da manufofin shugaban ƙasar Donald Trump.

An gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘No Kings’ a jihohin Amurka 50 har kusa da gidan Donald Trump a Florida, inda suke danganta Trump cewa yana nuna kamar shi sarki ne.

Masu zanga-zangar kenan a birnin New York Masu zanga-zangar na adawa ne da manufofin gwamnatin Trump na korar baki da kuma girke jami’an tsaro tare da korar ma’aikata.

karo na uku ke nan da ake hada gangami tun sake hawan Trump mulki a Fadar White House a watan Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *