Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki

0
1000171220
Spread the love

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce raɗe-raɗin juyin mulki da wasu kafofin yaɗa labarai ke ruwaitowa ba gaskiya ba ne.

Wata sanarwar da kakakin hedikwatar tsaron, Janar Tukur Gusau, ya fitar ta ce wasu kafofin yaɗa labarai na intanet ne suka ruwaito batun ta hanyar kafa hujja da soke faretin soji na ranar bikin ‘yancin kai, da kuma wasu jami’an rundunar da ake bincika da zargin karya ƙa’idar aiki.

“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa rahoton na ƙarya ne baki ɗayansa,” a cewarsa. “Dalilin da ya sa aka dakatar da faretin Ranar ‘Yanci shi ne saboda a bai wa shugaban ƙasa damar halartar wani taro a wajen Najeriya da kuma mayar da hankali wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yanfashin daji.

“Binciken da ake yi wa jami’ai 16 kuma irin wanda aka saba ne domin tabbatar da ɗa’a da ƙwarewar aiki. An kafa kwamatin bincike kuma za a sanar da sakamakon bincikensa.”

Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwar dakatar da faretin soji na al’ada da aka saba yi duk ranar bikin ‘yancin kai na ranar 1 ga watan Oktoba ba tare da wani takamaiman dalili ba.

Bayan bikin ne kuma rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar 4 ga watan Oktoba cewa ta tsare jami’an nata 16 bisa laifuka daban-daban da suka shafi rashin da’a da kuma karya ƙa’idar aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *