Al’ummar garin Kafin Soli sun yi zanga-zangar kisan Usman Kafinsoli ba bisa ka’ida ba.

Al’ummar garin Kafin Soli da ke karamar hukumar Kankia a jihar Katsina sun nuna rashin jin dadinsu kan kisan gillar da ‘yan kungiyar Katsina Community Watch suka yi wa dansu Usman Musa bisa wasu dalilai da basu saniba.
Katsina Community Watch wacce aka fi sani da ‘Katsina C-Watch, wata rundunar tsaro ce ta ‘yan jihar Katsina da gwamnatin jihar Katsina ta kafa domin magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a jihar.
Binciken ya nuna cewa, a ranar Asabar 11 ga Oktoba, 2025, wani lamari mai tayar da hankali ya afku wanda ya girgiza al’ummar Kafinsoli na kashe Usman Kafinsoli, da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Katsina C-Watch ne suka yi wa kisan gilla.
An gano cewar Usman ya rasa ransa ne bayan ganin sa a hannun ƴan ƙungiyar ta Katsina C-Watch akan hanyar su ta zuwa ofishin su sai dai kuma abin takaici bai dawo da rai ba.
Wannan lamarin ya haifar da tashin hankali a Kafin Soli inda wasu matasa da suka fusata suka tare duk wata babbar hanyar zuwa Dutsi-Ma, Matazu, Kankia da Charanchi suna kona tayoyi.
