Nnamdi Kanu na da lafiyar da zai iya fuskantar shari’a – Likitoci

Tawagar ƙwararrun likitoci a Najeriya, ƙarƙashin jagoranci shugaban ƙungiyar Likitocin ƙasar, sun tabbatar da cewa rashin lafiyar da aka ce na damun Nnamdi Kanu ba wata babbar damuwa ba ce.
Maishari’a, James Omotosho ne ya umarci tawagar likitocin ta duba lafiyar Kanu, bayan da lauyoyinsa suka yi iƙirarin cewa yana fama da wata jinya.
Cikin rahoton binciken tawagar ƙwararrun likitocin, da aka miƙa wa kotu ranar 13 ga watan Oktoban da muke ciki, ya ce rashin lafiyar da ke damun Kanu ba mai barazana ba ce.
Tawagar likitocin ta ce bayan auna lafiyar Kanu sun tabbatar da cewa za a iya ci gaba da yi masa shari’a, domin kuwa zai iya halartar kotu.
Bayan karɓar rahoton, Maishari’a Omotosho ya ce kotun ta gamsu da rahoton don haka za a ci gaba da shari’ar.
