Gwamnan Edo ya gargaɗi kwamishinoninsa kan rashin saka hular Tinubu

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya gargaɗi kwamishinoninsa game da rashin saka irin hular da shugaban Najeriya Bola Tinubu ke sakawa.
Mista Okpebholo ya bayyana haka ne a lokacin rantsar da wasu sabbin kwamishohinsa.
Yayin sa yake jawabi a wurin rantsar da kwamishinonin, Gwamna Okpebholo – wanda ke sanye da irin hular Tinubun – ya ce ba zai yafewa duk kwamishinan da ya je ofis ba tare da hular Tinubu ba.
”Kun ga wannan hular, ba zan yafewa duk wanda ya zo aiki ba tare da ita a kansa ba”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa ”indai ba kwat za ta saka ba, matsawar tufafin da za ka saka irin na al’ada ne da ke buƙatar sanya hula, to dole ku saka irinta”.
Gwamnan ya ce duk wanda ya saɓa dokar to zai koma gida.
