Hukumar NSCDC a Kano ta kama wanda ake zargin dillalin tabar wiwi, ta mika shi ga NDLEA

0
1000214084
Spread the love

Rundunar tsaro na farin kaya reshen jihar Kano ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargin dillalin tabar wiwi ne tare da mika shi ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin gudanar da bincike.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar, kwamandan jihar, Bala Bawa Bodinfa, ya ce kamen wani bangare ne na ci gaba da kokarin da rundunar ke yi na kawar da masu aikata laifuka a Kano.

A cewarsa, “A ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:30 na safe, jami’an NSCDC reshen Doguwa, da ke aikin leken asiri, sun kama wani direban babur tare da kama wani shahararren dillalin wiwi mai suna Yusuf Alasan, dan shekaru 25, dan asalin garin Doguwa, Muktar da Musa Sani, tare da wasu manya guda biyu.

Ya ce an kama wadanda ake zargin da manyan buhu uku cike da tabar wiwi, wadanda ake zargin suna jigilar su daga garin Doguwa zuwa Kafau a karamar hukumar Doguwa. “An kama su ne a kofar Riruwai,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *