Majalisar Gargajiya ta Lungunda ta Adamawa ta sanar da sauya suna zuwa Nungura

Majalisar Masarautar gargajiya ta Lunguda da ke karamar hukumar Guyuk a jihar Adamawa ta sanar da sauya suna daga yanzu za ta zama majalisar gargajiya ta Nungura.
An bayyana sabon sunan ne ta wata takardar rantsuwa da aka shigar a babbar kotun jihar Adamawa, inda ta tabbatar da sauya sunan daga “Lunguda” zuwa “Nungura.”
Ana ganin sabon sunan a matsayin yana nuna ainihi da tushen mutanen da suka kai sama da miliyan guda.
An samo sunan “Nungura” daga “Nungiraba,” ma’ana “mutanen da ke kusa da juna.”
Takardar shaidar da ke sanarda sabon sunan ta bayyana cewa “Lunguda,” wani turawan mulkin mallaka ne suka sa musu, wanda aka maye gurbinsa da “Nʋngʋra.”
