Gwmnan Jahar Enugu zai fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a mako mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar na kasa kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kudu-maso-Gabas Nentawe Goshwe Yilwatda da Emma Eneukwu ne suka bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a.
Shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya bayyana ficewar Mbah zuwa jam’iyya mai mulki yayin da yake rantsar da sabbin mambobin kwamitin riko na jihar Enugu karkashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar na jihar, Ben Nwoye, a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
Ana sa ran gwamnan zai bayyana sauya shekar sa a wani jadawalin taron da za a gudanar a jihar a mako mai zuwa.
Shugaban sabon kwamitin riko Nwoye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce gwamnan zai koma jam’iyya mai mulki tare da dukkan wadanda ya nada.
Akwai rade-radin cewa shi ma gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas na shirin komawa APC.
