Majalisar wakilai ta yi watsi da zargin kisan Kiristoci a Najeriya

0
1000211347
Spread the love

Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da iƙirarin da Amurka ta yi na cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya saboda addini, tana mai cewa wannan labari ba gaskiya ba ne kuma yana da ruɗani.

Majalisar ta kuma buƙaci a samu haɗin kai tsakanin diflomasiyya da hukumomin cikin gida wajen mayar da martani kan ƙudirin doka da ake shirin gabatarwa a Majalisar Dattawan Amurka, wanda ke neman a saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke take hakkin ‘yancin addini.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Okezie Kalu, da wasu ‘yan majalisa suka gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.

A kwanakin baya, ɗan majalisar Amurka, Sanata Ted Cruz, ya gabatar da ƙudiri domin kare Kiristoci a Najeriya daga abin da ya bayyana a matsayin cin zarafi da kisa saboda addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *