Zulum ya ba da kyautar gidaje ga ma’aikatan lafiya da malamai

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da kyautar gidaje ga ma’aikatan jinya da malaman makaranta 72 a ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar Borno a Najeriya.
Cikin waɗanda suka samu kyautar sun haɗa da wata ma’aikaciyar jinya ƴar ƙabilar igbo da ta kwashe fiye da shekara 24 tana aiki a jihar, Marbel Ijeoma Duaka.
Haka kuma gwamnan ya ɗauki ɗanta, Anthony aiki a jami’ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri.
Gwamnan ya miƙa gidan da kayan da ke cikinsa ga ma’aikaciyar, wadda ƴar asalin jihar Anambra ce, a ranar Talata.
Inda ya ƙara da cewa bata taɓa barin garin na Mafa ko da a lokacin da ake fuskantar hare-haren Boko Haram. Inda ya nemi ta ci-gaba da zama a jihar ko da bayan ta yi ritaya.
Nas ɗin ta miƙa godiyarta ga gwamnan kan abubuwan alherin da ya yi mata da kuma ɗanta.
