2027: Tinubu zai sha kaye idan Atiku da Jonathan suka fafata – Olarewaju

Babban mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan harkokin siyasa, Demola Olarewaju, ya ba da shawarar yadda shugaba Bola Tinubu zai fadi zaben shugaban kasa a 2027.
Olarewaju ya bayyana cewa idan Atiku da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan suka fito takarar shugaban kasa a jam’iyyu daban-daban a 2027, Tinubu zai fadi zabe.
Da yake amsa tambayoyi a kafar Mic On podcast a ranar Asabar, Olarewaju ya ce Jonathan zai samu goyon bayan mutane idan ya lashe zaɓen fidda gwani na firamare.
Da aka tambaye shi ko Jonathan zai fito a dandalin PDP, Atiku kuma ya fito a dandalin ADC, me zai faru da Tinubu, sai ya amsa da cewa: “APC zata sha kaye, APC ba za ta samu gindin zama ba a (zaben 2027) idan Jonathan ya fito a PDP, Atiku ko wani ya fito a ADC.”
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar PDP ba ta da karfi a siyasar kasa yanzu.
