Ban ce Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba – Jonathan

0
1000201118
Spread the love

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce an sauya wa kalaman da ya yi kan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ma’ana game da Boko Haram, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.

Yayin bikin ƙaddamar da littafin da tsohon babban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor ya rubuta, Jonathan ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa sanar da tsohon shugaban a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da take so ya shiga tsakani a tattaunawarta da gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin Jonathan.

Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari, ya musanta iƙirarin yana mai cewa wani ɓangare ne na ƙungiyar ya sanar da batun “wanda Buhari kansa bai san da shi ba”.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Jonathan ya fitar ta ce ya faɗi hakan ne kawai domin ya nuna irin dabarun da ƙungiyar ta dinga amfani da su a lokacin.

“Jonathan bai yi kalaman ba domin ya nuna cewa Buhari yana da wata alaƙa da Boko Haram, ko kuma yana goyon bayan su,” in ji sanarwar da Ikechukwu Eze ya fitar a yammacin yau Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *