Sojoji sun kama kayan ‘yan ta’adda a yankin Gubio

Dakarun Operation Hadin Kai sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke jigilar kayayyaki a kan hanyar Gubio-Binduldul ta jihar Borno.
Majiyoyi sun ce an kai farmakin ne a ranar 29 ga watan Satumba da sojoji suka yi.
Da suka ga sojojin, wadanda ake zargin sun yi watsi da babur dinsu uku dauke da abubuwan sha, kwai, shinkafa, da sauran kayayyaki.
An kama wani mutum daya da ake zargi yayin samamen.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa za’a kai kayan ne garin Abadam, sansanin ‘yan ta’adda.
