Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 42 da ake zargi da damfarar Intanet a Gashua

Jami’an hukumar shiyyar Maiduguri na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun kama wasu mutane 42 da ake zargi da damfarar yanar gizo a karamar hukumar Gashua ta jihar Yobe.
An kama su ne a wani samame da aka kai ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025 a wurare daban-daban a cikin Gashua, biyo bayan sahihan bayanan sirri kan yadda suke da hannu a laifukan da suka shafi kwamfuta.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da babura bakwai, motar Mercedes Benz daya, wayoyi hamsin da biyar (55) da kwamfutoci, da kuma playstation 5 (PS5) da playstation 4 (PS4) consoles.

Bayanan sirri da Hukumar ta samu na alakanta wadanda ake zargin da zamba daban-daban da suka shafi intanet.

Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
