Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dagacin kauye a Nijar

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Sarkin Fulanin Tungan-Madugu a gundumar Babanna da ke karamar hukumar Borgu a Nijar.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai farmaki gidan hakimin kauyen, Abu Bani-Gene mai shekaru 65 a safiyar ranar Lahadi inda suka kashe shi.
Daga bisani an kai gawarsa babban asibitin Babanna, inda aka ajiye ta domin tantancewa.
Jama’ar yankin sun ce ana shirye-shiryen binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da kokarin zakulo wadanda suka kai harin.
