Jam’iyyar PDP a Adamawa ta zabi Hamza Madagali a matsayin shugaban ta na jihar

0
1000188243
Spread the love

Wakilan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa sun zabi Alh Hamza Bello Madagali a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na jiha, inda Saleh Sheleng ya zama sakataren jam’iyyar, domin tafiyar da harkokin jam’iyyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Zaben wanda aka gudanar a yayin taron jam’iyyar na jihar a Yola ranar Asabar, an gudanar dashi cikin lumana da nasara karkashin jagorancin David Lorhenba, shugaban kwamitin shirya zaɓen.

A cewarsa, wakilai 2,656 daga kananan hukumomi 21 na jihar ne suka shiga tare da zabar sabbin jami’an zartaswa guda 39.

Ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyar kan yadda suke gudanar da ayyukansu cikin tsari.

A sakon nasa na bankwana, shugaban jam’iyyar mai barin gado Barr Attahiru Shehu ya taya sabbin shugabannin jam’iyyar murna tare da yin kira a gare su da su kara kaimi kan nasarorin da jam’iyyar ta samu.

Ya tuna yadda jam’iyyar PDP ta sauya sheka daga adawa zuwa mai rike da gwamnati karkashin jagorancin Ahmadu Fintiri wanda ya yi wa’adi biyu, kuma a cewarsa, ya gudanar da mulki mai tasiri.

A jawabinsa na karbar mulki, Hamza Madagali, wanda ya tashi daga sakataren tsare tsare zuwa shugaban jam’iyyar, ya nuna jin dadinsa da amincewa da aka yi masa.

Ya yi alkawalin salon jagoranci na bude kofa, wanda ya dora kan hada kai domin ciyar da Jam’iyyar PDP gaba a Jahar Adamawa dama Najeriya baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *