Gomnatin Adamawa ta fidda muhimmin sanarwa gameda daukan ma’aikata

Hukumar kula da ma’aikata ta jihar Adamawa na sanar da masu neman mukamin manyan jami’an zartarwa cewa an shirya gudanar da tambayoyin daukan aiki na tsawon kwanaki biyu domin tantancewa.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren dindindin, Abubakar Umar Maiha ya fitar, an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da adalci da kuma samar wa dukkan wadanda ke neman aikin dama a lokacin atisayen.
Masu neman aikin daga wasu kananan hukumomi da za’a bayyana za su bayyana a ranar Litinin, 29 ga Satumba:
Kananan hukumomin sun hada da
• Demsa
• Fufore
• Ganye
• Girei
•Gombi
• Guyuk
• Hong
• Jada
• Lamurde
• Madagali
Daga ranar Talata, 30 ga Satumba kuwa wadannan kananan hukumomin zasuyi nasu:
• Maiha
•Mayo-Belwa
• Michika
• Mubi Arewa
• Mubi ta Kudu
• Numan
• Shelleng
• Song
• Toungo
• Yola Arewa
• Yola Kudu
Ana shawartar duk masu nema da su lura da kwanakin su kuma su tabbatar da halartan kan lokaci.
