Gwamna Idris ya bayar da umarnin mayar da kudaden da aka cire daga albashin malamai

0
1000123950
Spread the love

Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya ba da umarnin mayar da kudaden da aka cire daga albashin malaman watan Satumba.

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen Jihar Kebbi, Murtala Usman, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

Ya ce Gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun koke daga kungiyar malamai ta Najeriya NUT game da cirar kudin da ba a bayyana dalili ba.

A cewarsa, wani bincike ya tabbatar da cewa an cire kudaden ne a matsayin kudin rajistar kwararru na hukumar rijistar malamai, TRC.

Ya kara da cewa Gwamnan ya gargadi ma’aikatar kudi da sauran hukumomi da su daina cire duk wani albashi ba tare da izini ba.

Shugaban kungiyar ta NLC ya yabawa Idris bisa gaggawar sa hannun da ya yi, inda ya ce hakan ya taimaka wajen dakile tashe-tashen hankulan ma’aikatu a jihar.

Ya kuma bukaci ma’aikatan da su rika kai kokensu ta hanyar kungiyoyinsu domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *