Gwamnatin Jihar Kebbi ta dakatar da hakan ma’adinai na wucin gadi a yankin Yauri

0
1000183811
Spread the love

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya bayar da umarnin rufe cibiyar hakar zinari ta Mararrabar Birnin Yauri na karamar hukumar Ngaski na wucin gadi.

Gwamna Idris ya ba da wannan umarni ne a wata ziyarar bazata da ya kai yankin a karamar hukumar Ngaski, biyo bayan rahotannin rashin fahimtar juna tsakanin al’umma da wakilan gwamnatin tarayya.

Dr Idris ya bayyana cewa an samu tashin hankali sosai sakamakon hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, inda a kwanan nan aka yi asarar rai guda a yankin.

Ya bayyana cewa babu wata gwamnati mai kishin kasa da za ta bari hakan ya ci gaba, yana mai cewa dole ne gwamnatinsa ta dawo da zaman lafiya tare da karfafa tsaro.

Gwamnan ya bayar da umarnin sakin wasu matasa kusan 50 da aka kama tare da tsare su a gidajen gyaran hali sakamakon rikicin da ya barke a baya-bayan nan da ya shafi hakar ma’adinai ta hanyar sasantawa a wajen kotu.

Tun da farko wakilin PAGMI Musa Adamu-Dantata da kwamishinan ma’adanai na Kebbi Garba Hassan-Warrah sun yi wa gwamnan bayanin wasu korafe-korafe da matsaloli a wurin hakar ma’adanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *