Rashidi Ladoja ya zama sabon Olubadan na 44

An naɗa tsohon gwamnan jihar Oyo Rasidi Adewolu Ladoja a matsayin sabon sarkin masarautar Ibadan Na 44.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na daga cikin manyan bakin da suka halraci bikin naɗin, da aka gudanar da fadar sarkin.
An gudanar da taron naɗin sabon sarkin ne a filin wasan Mapo inda jama’ar garin da baƙi da manyan baƙi tuni suka isa wurin domin halartar bikin naɗin.
Ladoja, mai shekara 81 ya zama Olubadan na 44, bayan shekaru masu yawa da fara zama Magaji.
Bayan ya zama Magaji a shekarar 1980, ya riƙa hawa matakai har ya kai matsayin Jagun Olubadan a shekarar 1993.
