Ma’aikatanmu na buƙatar makamai – Shugaban FRSC

Shugaban Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta Najeriya, (FRSC), Shehu Mohammed, bai wa jami’ansa makamai ne hanya guda ɗaya tilo da za ta tabbatar da dokokin tuƙi a kan manyan titunan ƙasar.
Yayin wata hira da gidan talbijin na ARISE NEWS ranar Alhamis, Mohammed ya bayyana irin hatsarin da ya ce jami’an hukumar na shiga a lokacin da suka gamu da masu ababen hawa.
Ya ce ta yaya jami’ai ƙalilan da ke sintiri za su iya dakatar da manyan tirelolin da aka yi wa lodi fiye da ƙima da kuma tankokin da ke ɗaukar kaya haɗe da gomman fasinjoji.
Shugabab na FRSC ya ce matsawar ba a bai wa jami’ansa abin da ya kira ”ƙarfin aiki” to zai yi wahala a iya tabbatar da dokokin tuƙi a ƙasar.
