Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin hajji

Tuni dai aka fara bayyana fargaba bayan da kasar Saudiyya ta bullo da wasu sabbin tsauraran ka’idoji ga maniyyata aikin Hajjin bana.
Saudiyya ta tsaya kai da fata wajen yin aiki da sababbin ka’idojin, wanda idan ta tabbata da yawa daga cikin maniyyatan Najeriya ba za su sami damar zuwa sauke farali a aikin Hajjin da ke tafe ba.
Yanzu haka dai wasu jami’an hukumar alhazan Najeriya suna kasar mai tsarki, domin tattauna yadda za a fuskanci sababbin matakan.
Fatima Sanda Usara, mai rikon mukamin daraktar yada labarai ta hukumar alhazan Najeriyar, wato NAHCON ce, ta shaida wa BBC cewa, babban matakin da Saudiyya ta dauka shi ne da zarar an daina karbar kudin aikin hajji, to ba za su koma baya ba, ama’ana babu wanda za a karbi kudinsa daga baya.
