An yanke wa tsohon shugaban Faransa Sarkozy hukuncin ɗauri

0
1000181152
Spread the love

Wata kotu a Faransa ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Nicolas Sarkozy hukuncin ɗauri na shekara biyar bayan samun shi da laifin haɗa baki wajen tafka laifi a wata shari’a da ta shafi karɓar kuɗaɗe daga tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi.

Sai dai kotun ta wanke shi daga sauran tuhume-tuhume a shari’ar wadda ta kasance mai sarƙaƙaiya.

Duk da cewa kotun ta wanke shi daga laifin karɓar kuɗi kai-tsaye daga Gaddafi a shekara ta 2007 domin gudanar da yaƙin neman zaɓe, ɗaya daga cikin alƙalan ya ce Sarkozy ya bar mutanen da ke kusa da shi sun yi wasu abubuwa na neman tallafin kuɗi domin yaƙin neman zaɓen nasa.

Sauran laifukan da aka wanke shi sun haɗa da rashawa da kuma amfani da kudin haram wajen yaƙin neman zaɓe.

Sarkozy ya yi zargin cewa shari’ar wani bi-ta-da-ƙulli ne na siyasa.

Masu shigar da ƙara sun zargi Sarkozy da yi wa Gaddafi alƙawarin wanke sunansa a tsakanin ƙsashen Yamma.

Sarkozy mai shekara 70 a duniya ya kasance shugaban ƙasar Faransa daga shekarar 2007 zuwa 2012.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *