Shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD karon farko tun 1967

Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria Ahmed al-Sharaa ya shaida wa babban taron Majalisar Dinkin Duniya cewa ƙasarsa ta sake ƙwato matsayinta a idon duniya.
Ahmed al-Sharaa ne shugaban Syria na farko da ya yi jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya tun shekarar 1967.
A watan Disamban da ya gabata ne, tsohon jagoran ƴan tawaye ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Al Sharaa ya ce yaƙin basasa ya ɗaiɗaita Syria, amma ya alƙawarta gudanar da zaɓuka a ƙasar.
Jawabin da ya yi a taron na New York ya ɗauki hankalin mahalarta taron a Amurka, ƙasar da a baya ta sanya tukwicin dala miliyan 10 ga wanda ya taimaka aka kama shi.
