‘Yan cirani za su jefa ƙasashen Yamma cikin mummunan hali – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasashen Yamma za su shiga cikin “mummunan hali” idan har ba su dakatar da kwararar ‘yan cirani ba.
Ya ce buɗe iyakoki ya zama babban ƙalubale, sannan ya zargi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da taimaka wa kwarar da baƙin hauren ke yi zuwa ƙasashen Yamma.
Kazalika, ya kuma yi watsi da batun hasashen sauyin yanayi da MDD ta yi, inda ya buƙaci a daina amfani da makamashi maras gurbata muhalli.
Tun da farko babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya ce duniya ta shiga wani zamani na ruɗani da rashin kwanciyar hankali mai saurin kawo wahalhalu marasa iyaka.
