An kwashe ‘yan Najeriya 145 da suka maƙale a Aljeriya

Hukumar bayar d aagajin gaggawa ta Najeriya Nema ta karɓi ‘yan Najeriya 145 da aka kwashe zuwa gida bayan sun maƙale a Aljeriya ranar Litinin.
Hukumar National Emergency Management Agency ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Legas da misalin ƙarfe 12:15 na rana a jirgin Air Algeria.
Nema ta ce ƙungiyar kula da ‘yan cirani ta International Organization for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin kwaso mutanen bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.
Mutanen sun haɗa da maza manya 132, da yara tara, da jarirai huɗu.
A ranar Alhamis da ta gabata ma aka kwaso wasu ‘yan Najeriya 148 zuwa gida bayan sun maƙale a Sudan, a cewar Nema.
