Darajar naira ta ɗan ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa

Darajar naira ta ɗan ƙaru bayan sanar da matakin Babban Bankin Najeriya na rage yawan kuɗin ruwa da maki 50 zuwa kashi 27 cikin 100.
Kazalika, shi ma farashin ɗanyen mai ya ɗan ƙaru zuwa dala 67.82 zuwa ƙarfe 5:00 na safiyar yau Laraba, inda ya ƙaru da santi 19 – ko kuma kashi 0.3 cikin 100 – kan kowace ganga ɗaya.
An canzar da nairar kan N1,487.36 kan dala ɗaya ranar Talata a kasuwar hukuma.
An rufe kasuwar canjin kuɗi ta jiya Talata nairar tana da ƙarin darajar kashi 0.08 idan aka kwatanta da 1,488.60 da aka canzar da ita kafin haka, kamar yadda bayanan CBN suka nuna.
