Tinubu bai da shirin tsawaita mulki bayan 2031 – Fadar shugaban ƙasa

0
1000119059
Spread the love

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ba shi da wani shiri na ci gaba da riƙe muƙamin shugaban ƙasar bayan Mayun 28, 2031, idan har aka sake zaɓensa a shekarar 2027.

Mai bai wa shugaba Tinubu shawara, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, a matsayin martani ga kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

A yayin wata ziyarar jaje daga tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a ƙarshen mako, El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da karkata zuwa mulkin kama karya, inda ya kwatanta Shugaban da Paul Biya na Kamaru, wanda ya shafe yana mulki tun daga 1982 har yanzu.

Sai dai Onanuga a mayar da martani ya bayyana cewa wannan magana ta El-Rufai ba ta da wani tushe bare makama.

Onanuga ya ƙara da cewa, “Shugaba Tinubu ɗan dimokuraɗiyya ne, kuma ba shi da wani shirin zama shugaban ƙasa har abada. Zai sauka daga mulki ne a ranar 28 ga watan Mayu, 2031 idan ya ci zaɓen 2027.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *