Shettima ya sauka birnin New York domin taron MDD

0
1000174523
Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya sauka a birnin New York ta Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga Satumba zuwa Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.

Shettima, wanda ke wakiltar Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabin Najeriya tare da shiga tattaunawar manyan jami’an MDD da kuma halartar wasu muhimman taruka a gefe.

A cewar ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, Najeriya na jagorantar ƙoƙarin samar da yarjejeniyar haraji ta duniya.

Wannan ne karo na biyu a jere da Shettima ke jagorantar tawagar Najeriya zuwa taron – bayan ya yi hakan a watan Satumban 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *