Likitoci sun gano tsutsa dake rayuwa cikin kwakwalwar mutane

Likitoci sun gano fararen tsutsotsi wato tapeworms a cikin kwakwalwar wani mutum da ke fama da matsanancin ciwon kai na ɓangare ɗaya da ake kira da Migraine.
Tsutsotsin suna naɗe kamar abin kama gashi.
Ana kyautata zaton cewa cin naman alade da bai dahu sosai ba da rashin wanke hannu a kodayaushe na iya kasancewa sanadin fitowar tsutsotsin.
Mutumin mai shekara 52 ya kasa jure ciwon kan nasa, lamarin da ya sa ya nemi likitoci bayan magungunan da aka ba shi ba su yi aiki ba.
Likitocin sun yi masa hoton kwakwalwa inda suka gano farar tsutsa da ke haddasa cutar ‘cysticercosis’.
