Gwamnatin Najeriya ta mayar da darasin tarihi a firamare da sakandare

0
1000166562
Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta sake mayar da darasin tarihi a matsayin darussan dole da ɗalibai za su dinga yi makarantun firamare da sakandare na ƙasar.

Wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar a yau Laraba ta ce an ɗauki matakin ne domin “ƙarfafa kishi, da haɗin kai tsakanin ‘yan ƙasa”.

“A karon farko ɗaliban Najeriya za su fara yin darasin tarihi tun daga aji 1 na firamare zuwa aji 3 na ƙaramar sakandare [JSS3], yayin da ‘yan aji 1 zuwa 3 [SS1 zuwa SS3] za su dinga yin darasin ilimin rayuwa da tsatso [Civic and Heritage Studies],” in ji sanarwar da ta wallafa a shafukan zumunta.

“‘Yan aji 1 zuwa 6 na firamare za su san asalin Najeriya, da gwanayenta, da shugabanni, da al’adu, da siyasa, da addini, da mulkin mallaka, da kuma mulki bayan samun ‘yancin kai.

“Ɗaliban JSS1-3 za su nazarci al’ummomi, da masarautu, da kasuwanci, da zuwan Turawa, da dunƙulewar Najeriya, da ‘yancin kai, da dimokuraɗiyya, da kuma ɗabi’un mutum.”

A shekarar 2007 ne gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sabuwar manhajar karatu, inda a ciki ta cire darasin tarihi daga firamare da sakandare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *