Gobara a Legas ta kashe ma’aikata 12 na FIRS da UBA

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nuna alhininsa dangane mutane 12 da suka rasa rayukansu a lokacin ibtila’in gobarar da ta tashi a dogon ginin Afritower a birnin Legas.
Gobarar wadda ta tashi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata ta shafi ginin hukumar tattara haraji ta FIRS da bankin UBA da kuma Capital UNited waɗanda dukkanninsu suke aiki a rukunin ginin.
Ofishin hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS da ke Legas ya tabbatar da rasuwar ma’aikatan nasa sakamakon tashin gobarar..
A cikin wata sanarwar da ofisihin ya fitar a shafinsa na X, ya ce bayan tashin wutar ne sai ma’aikata suka rinƙa durowa daga ofishin da ke hawa na bakwai al’amarin da ya sa wasu suka rasu sannan wasu da dama suka samu raunuka.
Duk da cewa hukumar ba ta faɗi adadin mutanen da suka mutu ko jikkata ba amma rahotanni na cewa waɗanda suka mutu sun kai mutum huɗu.
