Fasahar AI ta gano cutar da za ta kama mutane a shekara 10 masu zuwa

0
1000165613
Spread the love

Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu.

Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu ɗaya da ke barazanar kama mutum, tun ma kafin soma bayyana.

An wallafa cikakkun bayanan binciken – da suka bayyana da gagarumar nasara – a mujallar kiwon lafiya ta Nature.

An horar da fasahar AI ɗin ta hanyar amfani da bayanan lafiyar mutane dubu ɗari huɗu – da ba a bayyana sunayensu ba – a Birtaniya da Denmark.

Zuwa yanzu ba a soma amfani da fasahar ba, sai dai ana sa ran yin amfani da ita wajen gano cutuka da wuri a mutanen da suka fi barazanar kamuwa da cutuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *