Yara dubu 450 a Gaza za su fuskanci bala’i sakamakon mamayar isra’ila – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF, ya yi gargaɗin cewa sama da yara dubu 450 a Gaza za su fuskanci bala’i, sakamakon yadda mamayar sojin Isra’ila ke tsananta a yankin.
Daraktan asusun na yankunan gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika,Edouard Beigbeder, ne ya yi gargaɗin a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar juma’a, yana mai cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin na ci gaba da haifar da mummunan sakamako, wadda a cikin shekaru 2 bayanai suka tabbatar da cewa sama da Yara dubu 50 ne aka kashe ko aka nakasta.
Edouard, yace yanzu haka Yara na ƙarewa a yankin, inda ya kafa misali da Wesam mai shekaru uku, wadda ta tsira daga harin cikin dare da ya hallaka dukkan iyalanta a yankin Zeitoun.
Asusun na UNICEF ya yi gargadin cewa, wasu daga cikin yara dubu 2 da 400 da ke fama da matsanancin ciwon yunwa a yankin na Gaza waɗanda ake kula da su a halin yanzu, ka iya mutuwa da yunwa idan aka katse ba su magani.
