Amurka ta ce za ta mayar wa Brazil martani kan Bolsanaro

0
1000152864
Spread the love

Amurka ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani kan hukuncin da kotun kolin Brazil ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Jai Bolsonaro, bayan samun sa da laifin shirya yin juyin mulki bayan ya yi rashin nasara a zaɓen 2022.

An yanke wa Bolsonaro hukuncin zaman gidan yari na shakara 27.Mista Trump ya ce hukuncin da aka yanke wa abokin sa ya bashi mamaki kuma mummunan abu ne ga ƙasar.

Washington ta bayyana shari’ar a matsayin bita da kullin siyasa.

Lauyoyin Bolsonaro za su yi ƙoƙarin daukaka ƙara, duk da hakan zai yi wuya, ganin cewa alkali ɗaya ne kawai ya wanke shi daga laifin ba alkalai biyu da ake buƙata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *