Gwamna Idris ya dakatar da kwamishinan lafiya

0
1000123950
Spread the love

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya amince da dakatar da kwamishinan lafiya Yanusa Musa isma’il nan take.

Matakin ya biyo bayan umarnin da Gwamnan ya bayar ga Kwamishinan ya bayar da gamsasshiyar hujja kan zarge-zargen yin sakaci da yin watsi da aikinsa na hukuma.

A bisa wannan umarnin, an dakatar da Kwamishinan daga aiki har sai an sanar da shi.

Gwamna Idris ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da gaskiya, da’a, da kuma samar da ingantaccen aiki a dukkan bangarori, yana mai jaddada cewa dole ne jami’an gwamnati su tabbatar da amanar da aka yi masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *