Likitoci sun ƙara yin barazanar yajin aiki a Najeriya

0
1000082385
Spread the love

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙasar sabon wa’adin kwana ɗaya ta biya buƙatunta, bayan ƙarewar na kwana 10 da ta bayar a baya, wanda ya ƙare a ranar 10 ga watan Satumba.

Shugabannin ƙungiyar sun ɗauki wannan matkin ne a ƙarshe taron da suka yi a ranar Laraba.

Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a gagauta aiwatar da matakan da aka yi masu alƙawari.

A wata sanarwar da ƙungiyar ta bitar a ranar 1 ga watan Saumban bana, ta nemi a gaggauta biyan ƴaƴanta bashin ƙarin albashinsu na wata buyar da suke bi, bayan aiwatar da ƙarin kashi 25 zuwa 35 na tsarin albashin ma’aikatan lafiya.

Lkitocin sun kuma abatar da wasu buƙatun da suka haɗa da gagauta biyan su bashin alawus-alawus ɗinsu da kuma sauran buƙatu.

Likitoci masu neman ƙwarewar aiki a Najeriya su ne ƙashin bayan aikin kiwon lafiya a ƙasar, inda suke gudanar da ayyuka asibitoci mallakin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.

Duk lokacin da suka shiga yajin aiki ana samun koma baya wajen kiwon laiyar al’umma, lamarin da ke jefa rayuwar marasa lafiya ciki halin rashin tabbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *