Gwamnati ta gurfanar da ƴan ƙungiyar Ansaru biyu da aka kama

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar Ansaru, wata kungiyar tsageru kuma gawurtattun ƴanbindiga mai alaƙa da Al-Qaeda, a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis.
Shugabannin ƙungiyar Ansarun biyu sun hada da Mahmud Muhammed Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas Mukhtar, da mataimakinsa, Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Isah Adam/Mahmud Al-Nigeri.
Ana zargin su da aikata laifuka manyan 32 masu alaƙa da ta’adanaci.
Hukumomin Najeriya na zarginsu da taimakawa da kuma haɗa kai wajen aikata laifukan ta’addanci, tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015 da kuma kitsa harin gidan yarin Kuje da aka yi a shekarar 2022 da hari a wajen haƙar ma’adinin uranium na Nijar da garkuwa da wani Bafaranshe mai suna Francis Collomp a Katsina da sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba a shekarar 2019 da sace Sarkin Wawa
.Haka kuma suna da alaƙa da ƴanbindiga a yankin Maghreb, musamman Mali da Nijar da Burkina Faso kamar yadda mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar kwanakin baya.
