Mun kai hari Doha ne domin kawar da Shugabannin Hamas dake Qatar

0
1000146457
Spread the love

Isra’ila ta ce ita ce ta kai hari kan shugabannin Hamas a Doha, babban birnin Qatar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Isra’ila ta ce: “Dakarun IDF da na ISA sun ƙaddamar da harin kai-tsaye” kan shugabannin ƙungiyar Hamas.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “A tsawon shekaru, waɗannan shugabanni na Hamas sun jagoranci ayyukan soji na ƙungiyar, kuma suna da hannu dumu-dumu a cikin mummunan kisan kiyashi da aka yi a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma sun ci gaba da kitsawa da tafiyar da yaƙin da ake yi da Isra’ila.

“Kafin ƙaddamar da harin, an ɗauki matakan kauce wa cutar da fararen hula, ciki har da yin amfani da makaman da ba sa kuskure da kuma ƙarin bayanan sirri,” a cewar sanarwar”

Rundunar IDF da abokiyar aikinta ISA za su ci gaba da yin aiki kan jiki kan ƙarfi domin murƙushe ƙungiyar wadda ke da alhakin kai harin ranar 7 ga watan Okotoba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *