Iran ta yi Allah wadai da harin Isra’ila ta kai Qatar

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai birnin Doha na ƙasar Qatar.
Yayin da yake jawabi ta gidan talbijin na ƙasar, kakakin ma’aikatar, Esmail Baghaei ya ce harin ya ”saɓa wa dokokin duniya”, sannan ya keta mutuncin ƙasar Qatar da masu tattaunawar sulhun”.
Ya ƙara da cewa dole matakin ya zama ”kyakkyawan gargaɗi ga ƙasashen yankin da ma duniya baki-ɗaya”.
A ƙarshen watan Yuni ne Iran da Isra’ail suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da suka yi na kwana 12.
