Manoman Albasa sun yi asarar N1bn saboda rashin ingancin iri a Jigawa

Manoman Albasa a jihar Jigawa sun yi asarar amfanin gona da ya kai kusan Naira biliyan 1 sakamakon amfani da iri mara inganci a lokacin damina ta bara.
Shugaban kungiyar manoman Albasa ta Jigawa Malam Dauda Marma ne ya bayyana haka a wata hira da gidan rediyon jihar Jigawa.
Ya bayyana cewa wasu ‘yan kasuwa marasa gaskiya sun raba irin albasa da aka shigo da su daga kasar Maroko ga manoma, wanda hakan ya janyo hasarar dimbin arziki na manoma da yawa.
A cewarsa, an kawo irir ne a jihar ta jihohin Kebbi da Yobe.
Malam Dauda ya yi gargadin cewa a gaba duk wanda aka samu yana sayar da iri mara inganci a Jigawa za a hukunta shi gwargwadon yadda doka ta tanada.
