Ko kun san garin da mata kawai ake bari su zauna a ciki?

Garin Noiva do Coideiro dake kasar Brazil wani dan karamin Gari ne wanda ke dauke da mata zalla akalla 600/700 dukan wadanda ke cikin wannan gari dai mata ne ba maza.
Dalilin kuwa duk mazajen garin ba’a barin su su zauna sai dai su dinga zuwa hutun karshen mako kamin su sake komawa aikin su a birni idan kuma kai yaro ne kana kaiwa shekara 18 za’a ce ka tafi birni ka bar musu gari, sai dai kuma a shekarun baya sun taba kukan cewa suna bukatar mazaje domin suyi aure amma bisa wancan sharadin na zuwa karshen mako mazajen basa zuwa.

Dalilin dokar kuwa shi ne, wata mata da ta fara zama a garin wacce aka koreta daga asalin garin su sakamakon zarginta da aikata wani abun kunya a garin saboda haka aka koreta daga garin wanda hakan yasa ita da sauran danginta suka tattara suka koma wannan garin na Noiva do Cordeiro inda suka sa dokar hana maza zama a ciki don gudun sake samun irin sharrin da aka yiwa kakar tasu na aikata lalata.
