Sojoji 45 ne suka yi batan dabo a Colombia
70208015. Bogotá, 8 Feb. 2017 (Notimex-Presidencia de Colombia).- Ondeando la bandera de la paz, guerrilleros de las FARC marchan hacia un campamento donde se sumarán a la reconciliación y al desarme tras más de cinco décadas de conflicto, el cual termina gracias a los acuerdos de paz. NOTIMEX/FOTO/PRESIDENCIA DE COLOMBIA/COR/POL/

Rundunar sojin Colombia ta ce akalla sojoji 45 aka sace a yankin da wani bangare na tsohuwar kungiyar ‘yan tawaye ta FARC ke iko da shi.
An sace sojojin ne a yayin da suke wani aiki a yankin Cauca. Ministan tsaron Colombia, Pedro Sanchez, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ana zargin daruruwan mutane da hannu a sace jami’an sojin.
Ya ce dukkan wadanda aka samu da satar sojojin za su dandana kudarsu.
Cauca dai yankin ne da ake noma Coca wadda ake amfani da ita wajen hada hodar ibilis.
