Ma’aikatan Najeriya na buƙatar ƙarin mafi ƙarancin albashi daga naira 70,000

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya wato NLC ta ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta sake duba yiwuwar ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙasar, domin a cewarta, naira 70,000 ya yi kaɗan a yanzu da tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare.
A watan Yulin bara ne dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu a sabuwar dokar ƙara mafi ƙarancin albashi, inda ya ƙara ƙaramin albashi na ma’aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, duk da cewa wasu jihohin na biyan sama da haka.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito ƙungiyar na cewa hauhawar farashin kayayyakin buƙata a ƙasar ne ya sa mafi ƙarancin albashin naira 70,000 ba ya isar ma’aikacin ƙasar gudanar da abubuwan da suke buƙata na rayuwar yau da kullum, kamar yadda muƙaddashin babban sakataren NLC, Mr Benson Upah ya shaida wa NAN a ranar Lahadi a Abuja.
