Bana fargabar Trump ya ƙaƙabawa Najeriya takunkuman haraji – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa ƙasar ba ta fargabar matakan da shugaban Amurka Donald Trump ke ɗauka na ƙaƙaba haraji wanda tuni duniya ta fara ganin tasirinsa bayan haddasa naƙasu ga tattalin arziƙin ƙasashe.
Kalaman na Tinubu na matsayin martani kan kiran da Trump ke ci gaba da yi wajen ganin ƙasashe masu arziƙin man fetur sun ƙara yawan man da suke fitarwa kasuwannin duniya don karya farashinsa, inda shugaban na Najeriya ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Afrika ke cewa tuntuni suka daina dogaro kacokam da sashen na fetur.
A cewar shugaba Bola Tinubu na Najeriyar, kuɗaɗen da ƙasar ke samu a ɓangaren da ba na man fetur ba kaɗai, sun isa su riƙeta tare da ƙalubalantar duk wasu haraji da Amurkan ka iya lafta mata.
Tun bayan hawansa karagar mulki, shugaba Trump ya gabatar da sabbin harajin kasuwanci da suka birkita hada-hadar ƙasashe da dama ciki har da Najeriyar, lamarin da Bola Tinubu ke cewa sam ba zai yiwa ƙasar illa kamar yadda ake hasashe ba, domin kuwa ƙasar na da tarin ɓangarorin da za su kangeta daga ganin tasirin harajin.
